Gwamantin tarayya ta sanar da ware tallafin Naira Biliyan biyar ga ko wacce jiha har da birnin tarayya Abuja.
Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan zaman majalisar tsaro daya gudana, wanda mataimakin shugaban kasar Kashim Shettima ya jagoranta.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Yace mataimakin shugaban kasar Kashim Shettima ya tabbatar musu da cewa Gwamnatin tarayyar ta ware kudin ne a wani bangare na rage radadi ga Al’ummar Nijeriya bisa cire tallafin man fetur da tayi.
Majalisar da ta kunshi Gwamnonin jihohi 36, Gwamnan babban bankin kasa na CBN da kuma wasu kusoshin Gwamantin tarayya Nijeriya.
PRNigeria hausa












