Home Labarai Tinubu ya nada shuwagabannin NTA, VON, FRCN

Tinubu ya nada shuwagabannin NTA, VON, FRCN

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya nada Sabbin shuwagabanni hukumomi da ma’aikatun 8 dake karkashin hukumar sadarwa da wayar da kai ta kasar.

Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da mashawarci kan yada labarai ga shugaban kasar Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu a birnin tarayya Abuja.

Sanarwar tace an nada: According to the statement those appointed are:

(1). Mr. Lanre Issa-Onilu matsayin shugaban hukumar wayar da kai ta (NOA)

(2) Mr. Salihu Abdulhamid Dembos matsayin shugaban gidan Talabijin na kasa  (NTA).

(3) Dr. Muhammed Bulama matsayin shugaban gidajen Radio Gwamantin Tarayya  (FRCN).

(4) Mr. Charles Ebuebu matsayin shugaban hukumar dake lura da kafafen yada labarai na Nijeriya (NBC).

(5) Mr. Jibrin Baba Ndace matsayin shugaban kafar yada labarai ta  (VON)

(6) Dr. Lekan Fadolapo shugaban hukumar dake lura da tallace-tallace a kafafen yada labarai ta (ARCON).

(7) Mr. Ali Muhammed Ali matsayin shugaban kamfanin dillancin Labarai na Nijeriya News (NAN).

(8) Mr. Dili Ezughah matsayin shugaban (NPC).

Sanarwa ta bayyana cewa Tinubu ya bukaci sabbin shuwagabannin dasu zama masu amfani da fikira wajen ciyar da inda aka dora musu nauyin lura dashi gaba, tare da jagorori na kwarai.

Ta kuma cewa nadin nasu ya fara aiki nan take.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp