Babban Mai Temakawa Shugaban Ƙasa a Kan Harkokin Yaɗa Labari da Hulɗa da Jama’a. Tope Ajayi, ya ce, babu wani shirin da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu take yi na dawo da tallafin man fetur.
Ajayi ya yi wannan bayani ne a yau Alhamis a shafinsa na X wanda a baya ake kira da Twitter da misalin ƙarfe 6:08 agogon Najeriya.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ya rubuta cewar, babu wani shiri na dawo da duk wani Nau’I na tallafi, sannan kuma babu wani yanayi da zai sa a goyi bayan duk wani tashin farashin a wannan lokacin.
Ya ƙara da cewar, Shugaban Ƙasa Tinubu ya gamsu da cewar, bisa bayanan da yake samu, za a iya ci gaba da kasancewa kan farashin da ake kai a yanzu haka.
Wannan rubutu na Ajayi dai ya zo ne, biyo bayan labaran da suke cewa, an ɗan dawo da tallafin man fetur saboda ƙaruwar kuɗin shigo da shi wanda ya samo asali daga faɗuwar darajar naira.












