Dr. M.D Hassan ya dauki nauyi Daliban jihar kano 50 a fannin karatun Lafiya

Gwamnatin jihar Kano ta ce, za ta rubanya kokarin da ta ke na inganta harkar Ilimi a  jihar  dake arewa maso yammacin Nijeriya dan ganin an samu Al’umma ta gari.

Gwamnan jihar Injiyiya Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin taron bayar da tallafin karatun gaba da sakandire a makarantun lafiya ga daliban karamar hukumar Nassarawa 50 da Hon. Muhammad M.D Hassan ya dauki nauyi, domin koyi da tsarin da gwamnatin jihar kano ke kai

Da yake jawabi Gwamnan jihar kano wanda ya sami wakilcin mai taimaka masa  na musamman a fannin harkokin lafiya Hon Ali Chiranchi, ya ce “daman na daga cikin kudirce-kudirce Gwamnatin Abba, na samar da Ingantaccen Ilimi a jihar Kano”, inda ya kuma ja hankalin daliban da su kasance masu maida hankali akan karatun su.

A nasa jawabin Hon. Muhammad M.D Hassan, wanda shi ne wanda ya dauki nauyin Daliban zuwa makarantun Lafiya, yayin zantawar sa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron bayar da tallafin ya ce,  “mun dauki nauyin daliban ne domin kara jaddada aniyar mu na samar da ci gaban Al’umma, kamar yadda Engr. Rabi’u Kwankwaso ya dora mu a kai”.

Sannan Hon. Muhammad M.D, ya ce tallafin karatun na a fannin lafiya, zai ci gaba da kasancewa lokaci zuwa lokaci, dan ganin an ragewa Gwamnati nauyin Dalibai ‘yan asalin Kano dake kan ta.

Tallafin karatun na lafiya dai ya sanya daliban cikin farin duba da yadda suka gaza bayyana farin cikin su, kamar yadda wasu daga cikin daliban suka bayyana.

Harkar Ilimi a Nijeeria dai na daya daga cikin abubuwan dake ciwa Al’ummar kasar tuwo a kwarya wanda hakan ne ma tasa, Gwamnatin Kano, ta dauki nauyin Karatun Dalibai 1001 zuwa kasashen ketare.

A makon da ya gabata ne dai Daliban da Gwamnatin jihar Kano kar-kashin jagorancin Abba Kabir Yusuf, ta tura karatu zuwa kasashen waje, suka fara tashi zuwa makarantun da za suyi karatu.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 14 hours 14 minutes 50 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 15 hours 56 minutes 15 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com