Tinubu zai fara biyan sabon tsarin mafi karancin albashi.

Gwamnatin Najeriya ta ce sabon tsarin mafi karancin albashi zai fara aiki daga ranar ɗaya ga watan Afrilun 2024.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na kasar, Idris Mohammed, wanda ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da manema labarai a Abuja, ya ce tsarin mafi ƙarancin albashi na naira 30,000 na yanzu zai daina aiki ne a karshen watan Maris na shekarar 2024.

Mohammed ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, yayin nazarin kasafin kudi na shekarar 2024-2026 da shugaba Tinubu ya gabatar inda ya ce za a kashe naira tiriliyan 24.66 kan albashi a shekarar 2024 da 2025 da kuma 2026.

Bayan cire tallafin man fetur da Tinubu ya yi a ranar 29 ga watan Mayun 2023, gwamnatin tarayya ta amince ta bai wa kowane ma’aikacinta tallafin naira 35,000 domin rage raɗaɗin cire tallafin.

Sai dai kungiyar ƙwadago ta dage kan cewa tallafin naira 35,000 na wucin-gadi bai wadatar ba, inda ta kara da cewa ya kamata a sake duba mafi karancin albashi a shekarar 2024.

Tawagar Gwamnatin Tarayya da Majalisar Tattaunawar Ma’aikata ta Kasa a ranar 18 ga Oktoba, 2019, sun amince da aiwatar da mafi karancin albashi na naira 30,00 bayan shafe watanni ana tattaunawa.

Sai dai a ranar Alhamis kungiyar kwadago ta tabbatar da cewa ta fara tattaunawa da gwamnatin tarayya, inda ta kara da cewa bisa tsarin dokar kwadagon kasar ya kamata a sake duba mafi karancin albashi duk bayan shekaru biyar.

Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya, Joe Ajaero, ya ce kwanan nan, “Sake duba mafi ƙarancin albashi na kasa lamari ne na doka da ake sa ran zai faru a 2024.”

A nasa ɓangaren, ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed, ya shaida  cewa, ƙarin albashin na da nufin maye gurbin matakin wucin-gadi da gwamnati ta sanya don magance wahalhalun da ke tattare da cire tallafin man fetur.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 9 hours 44 minutes 49 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 11 hours 26 minutes 14 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com