Home Labarai sojojin Nijeriya sun hallaka ‘yan bindiga a jihar Sokoto

sojojin Nijeriya sun hallaka ‘yan bindiga a jihar Sokoto

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta hallaka wasu ‘yan bindiga tare da kuɓutar da wasu mutane da suke garkuwa da su a jihar Sokoto.

Cikin wani saƙo da rundunar sojin ƙasar ta wallafa a shafinta na X, ta ce cikin wani hari da dakarunta na Hadarin Daji suka kaddamar a kauyen Bauni da dajin Bauni a jihar ranar 14 ga watan Disamba, inda sojojin suka shafe sa’o’i masu yawa suna musayar wuta da ‘yan bindigar.

Sanarwar ta ce bayan da sojojin suka matsa wa ‘yan bindigar, sai suka tsere tare da barin maɓoyarsu, lamarin da ya sa sojojin suka samu nasarar kuɓutar da mutum shida da suke garkuwa da su.

”Sai dai kafin tserewar ‘yan bindigar, sojojin sun kashe uku daga cikinsu, tare da gano makamai”, in ji sanarwar.

Makaman da aka gano sun haɗar da bindiga ƙirar AK-47 biyu da kuttun adana alburusai 19, da alburusai, da bindigogin toka biyu d babura, da na’urorin oba-oba da sauran kayayyaki

Sanarwar ta ce sojojin sun lalata maɓoyar ‘yan bindigar tare da babuwarn da suka gano nan take.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp