Kotun Ƙolin Najeriya ta sanya ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba domin sauraron ƙarar da aka shigar kan zaɓen gwamnan jihar Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP na kalubalantar hukuncin kotun daukaka ƙara da ta tabbatar da hukuncin kotun sauraran ƙararrakin zabe da ta soke nasararsa tare da bayyana Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar na ranar 11 ga Maris.
Wannan ne karon farko da kotun za ta fara zama, inda za ta fara jin bahasi, yayin da har yanzu akwai muhimman takardun da ba a kai wa kotun ba.
Read Also:
Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukuncin cewa Gwamna Yusuf ba dan jam’iyyar NNPP ba ne a lokacin da ya tsaya takarar gwamna.
Amma tabbataccen kwafin hukuncin, wanda ya bayyana kwanaki kaɗan bayan zaman kotun, ya kunshi bayanai masu karo da juna game da hukuncin da ya janyo ce-ce-ku-ce.
Duka bangarorin biyu dai sun yi ikirarin cewa hukuncin ya tabbatar da nasarar da suka samu a zaben.
Sai dai jam’iyyar NNPP ta shigar da ƙara a gaban kotun ƙoli, inda take ƙalubalantar hukuncin kotun daukaka ƙara da ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamna.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 32 minutes 4 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 13 minutes 29 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com