Rundunar ‘yan sandan jihar katsina ta tabbatar da mutuwar mutane hudu, inda takwas suka bata sakamakon harin ‘yan bindiga a wasu garuruwan jihar.
kakakin rundunar ASP Abubakar Aliyu ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce ‘yan bindigar sun aukawa wasu manoma a kayukan Dantsuntu da Nahuta a karamar hukumar batsari, in da suka hallaka mutane 4.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
yayin da yake ganawa da manema labarai ASP ALiyu yace tuni rundunar ‘yan sanda ta sami labarin aukuwar lamari, haka kuma ya tabbatar da batan mutane 4 sakamakon harin ‘yan ta’addan.
wani daga cikin wadanda suka kubuta daga harin, wanda ya bukaci a sakaye sunan sa ya ce harin na daga cikin hare haren da ‘yan bindigar suke kaiwa kauyuka, wanda hakan ke haifar musu da shiga mawuyacin hali wajen gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum, wanda hakan baya barin su zuwa gonakin su.
PRNigeria Hausa












