Home Labarai Sanatocin Nijeriya sun yi Alla wadai da harin jihar Filato

Sanatocin Nijeriya sun yi Alla wadai da harin jihar Filato

Kungiyar sanatocin Arewa ta yi Allah-wadai da kashe-kashen mutane da ake yi a jihar Filato, inda suka bukaci hukumomin da abin ya shafa su fara bincike.

Kakakin kungiyar, Sanata Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila a wata sanarwa da ya fitar, ya ce babu shakka Sanatocin Arewa sun yi Allah-wadai da munanan ayyukan kashe-kashe al’umma a jihar ta Filato.

Kawu ya kara da cewa, Sanatocin sun jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa, da ‘yan uwa, da jama’a, da kuma gwamnatin jihar Filato.

“Abun da ya faru tabbatar abun bacin rai ne, kuma mun tsaya tsayin daka kan kudurinmu na neman adalci. A matsayinmu na yan majalisa, muna yin Allah wadai da wannan mummunan aiki, muna kuma kira ga hukumomi da su gaggauta fara gudanar da cikakken bincike.

Bayar da kayan aikin da suka dace don gudanar da bincike da nufin ganowa da kuma kamo masu laifi shi ne mafi mahimmanci. Masu laifin dole ne su fuskanci hukuncin, tare da tabbatar da adalci.

a kara da cewa Sanatocin basu ji dadin faruwar wannan lamarin ba a cikin wannan mawuyacin yanayi, hadin kan ‘yan kasa na da matukar muhimmanci, yana mai cewa “a matsayinmu na wakilan jama’a, muna kira ga gwamnatin tarayya da ta hada rahoton bincike na wannan lamari, ta kuma dauki matakin da ya dace don hana afkuwar hakan a nan gaba.

PRNigeria Hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp