Tsohon kakakin majalisar wakilan Nigeria, Ghali Umar Na’Abba, ya rasu a Abuja yana da shekaru 65 a duniya.
Mai taimaka wa marigayin Ahmed Tijjani Lawal ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a wata tattaunawa ta wayar tarho ranar Laraba.
Read Also:
Ya ce kakakin.majalisar ta 8 ya rasu ne da sanyin safiyar Laraba a babban asibitin kasa dake Abuja.
Na’Abba ya zama dan takarar jam’iyyar PDP a zaben yan majalisar wakilai ta kasa a watan Afrilun 1999 a mazabar Kano Municipal dake jihar Kano .
Ya rasu ya bar mata daya, da ’ya’ya 10, da jikoki uku.
PRNigeria hausa