Shuwagabannin Kananan hukumomin Kano 44 sun Maka Gwamnatin jihar a gaban kotun tarayya Bisa Zargin ta da Kokarin dibar kudinsu Domin Tayi Aikin Wasu Gadoji a birnin jihar.
A ta cikin takardar Karar mai Lamba FHC/ABJ/CS/1733/2023, Shuwagabannin Kananan Hukumomin Sunyi Karar Gwamnatin Kano ne, Da Kwamishinan Shari’a Na jihar dama Akanta Janar na jihar.
Read Also:
Wannan na matsayin wani matakai kan yunkurin gwamnatin jihar na taba musu kudadensu na cikin asusun hadaka da sukeyi da ita (Joint Account) sakamakon abinda sukace ana kokarin dibar kudin a aikin gadojin Dan Agundi da ta Tal’udu.
Takardar mai Dauke da Kwanan Watan Jumu’a 29 Ga Watan Disambar ta Roki Kotun Data Hana Gwamnatin Kano Taba musu Kudin domin yin aikin gadojin Guda Biyu.
PRNigeria ta tabbatar da ganin ya Shirye-Shiryen Gwamnatin Kano yayi nisa Wajen Fara ayyukan Guda Biyu.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 41 minutes 35 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 23 minutes 0 second
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com