Home Labarai Abba Gida-gida ya kaddamar da ayyukan sabbin gadoji

Abba Gida-gida ya kaddamar da ayyukan sabbin gadoji

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya aza harsashin ginin gada mai hawa uku da zata lashe Naira biliyan 27  a mahadar Dan’agundi, da kuma Tal’udu duk a cikin birnin Kano.

Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labaran gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin tofa ya fitar kuma aka raba manema labarai a jihar.

A yayin a aza harsashin ginin, gwamnan ya ce an fara gudanar da manyan ayyukan ne domin rage cunkoson ababen hawa, da saukaka zirga-zirga, da kawata birnin, da hana gurbatar muhalli, da samar da ababen more rayuwa ga al’umma.

Haka Kuma gwamnan ya nanata alkawuran gwamnatinsa na samar da ababen more rayuwa a jihar tare da kudurin samar da karin ribar dimokuradiyya musamman ga wadanda aka zalunta.

Ya ce  matsayin jihar na babban birni ta cancanci a samar da gagarumin sauyi na ababen more rayuwa domin biyan bukatun mazauna birnin sama da miliyan goma da inganta zamantakewa da tattalin arzikin mazauna birnin.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Tarayya ta Kaddamar da Kwamitin Bincike Kan Mutuwar Ma'aikatan Haƙar Ma'adinai 37 a Hukumar Kula da Haƙar Ma'adinai ta NSCDCMajalisar Dattawa ta 10 da Ma'anar Jagorancin Majalisa Daga Kabir AkintayoDarakta Janar na NITDA ya yi Kira da a Hada Hannu Kan Tsarin AI a Taron Manyan ShugabanniƳancin Sanin Gaskiya: Bayani Game da Tsarin Gudanar da Harkokin Sadarwa na Najeriya Daga Franklyn Ginger-EkeHOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna Yusuf
X whatsapp