Rundunar ƴan sanda a jihar Nasarawa ta ce sun ceto wani malamin jami’ar jihar da ke Keffi, Isaac Igbawua daga hannun masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.
wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin ƴan sandan jihar, Ramhan Nansel ya fitar aka kuma raba manema labarai
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ya ce jami’an rundunar ce tare da haɗin gwiwar ƴan bijilanti suka kuɓutar da malamin a wani kauye mai suna Ogba, a karamar hukumar Nasarawa Eggon da ke jihar.
An sace Igbawua, wanda malami ne a sashin kimiyyar ƙananan halittu (Microbiology) ranar 27 ga watan Disamba a karamar hukumar Kokona.
Kwana guda bayan sace shi, rundunar ƴan sandan jihar ta Nasarawa ta kama wani ɗalibin Jami’ar Tarayya da ke Lafiya, Daniel Favour Chukwuebuka, tare da kwato bindiga da harsashi a wajen da yake zama.
PRNigeria Hausa












