Hukumar dake hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar Kano NDLEA, tace ta samu nasarar cafke mutane 1,016 da ake zargin su da tu’ammali da miyagun kwayoyi a cikin shekarar 2023 da muka yi bankwana da ita.
Mai magana da yawun hukumar Sadiq Muhammad Maigatari shi ne ya bayyana hakan, inda yace mutanen da aka kama sun hadar da mata guda 40.
Read Also:
Kazalika yace sun samu nasarar kama tan sama da 9,000 na miyagun kwayoyin duka dai a cikin shekarar.
Maigatari ya yaba da kokarin jami’an hukumar, inda yace suna daukar kwararan matakai wajen kawar da dukkanin wani nau’i na tu’ammali da miyagun kwayoyi a fadin Kano, domin samar wa da al’ummar jihar zaman lafiya da kwanciyar hankali.
PRNigeria hausa