Wasu mutane sanye da kakin soji da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe mutane 12 a kauyukan Tsiha da kuma Gatamarwa da ke karamar hukumar Chibok a jihar Borno, Najeriya.
Mazauna kauyukan sun bayyana manema labarai cewa maharan sun dinga harbin mai uwa-da-wabi, lamarin da ya kai ga mutuwar mutanen, sannan suka yi awon gaba da mutum guda.
Read Also:
Rundunar ‘yan sandar jihar ta ce an samu gawarwakin mutanen da suka rasa rayukansu a harin.
Yayin da kuma ta fara bincike kan lamarin domin gurfanar da wadanda ake zargi da kai harin.
Bayanai sun nuna cewa maharan masu yawan gaske sun aukawa kauyukan ne a ranar Litinin da ta wuce.
PRNigeria hausa