Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da sanarwar rage yawan jami’an da za su riƙa yi masa rakiya a duk tafiye-tafiyen aiki da zai je a ciki da wajen Nijeriya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai bashi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai ranar talata.
Matakin ya shafi dukkan ministoci da manyan jami’an gwamnatinsa ciki har da mataimakin shugaban ƙasa da uwargidan shugaban ƙasa.
Read Also:
Sanarwar ta bayyana cewa matakin, wani yunƙuri ne na rage yawan kuɗaɗen da jami’an gwamnati ke kashewa kan harkokin tafiye-tafiye.
Ta ce yawan jami’an da za su riƙa yi wa shugaban ƙasa rakiya zuwa ƙasashen waje, nan gaba ba za su wuce jami’ai 20 ba. Haka zalika, Ngelale ya ce Tinubu ya ba da umarnin a daina tura ɗumbin jami’an tsaro zuwa wata jiha a duk lokacin da zai kai ziyara can, maimakon haka za a riƙa amfani da jami’an tsaron da ke jihar ne kawai don tabbatar da tsaro.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 8 hours 17 minutes 12 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 9 hours 58 minutes 37 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com