Hukumar EFCC ta sake waiwayar binciken halasta kuɗaɗen haram na wasu tsofaffin gwamnoni 12 da wasu ministoci da suka gabata, kuma adadin kuɗin ya haura naira biliyan 853.b.
Jaridar Punch ta gano cewa adadin kuɗin da ake nema daga wajen wasu manyan tsofaffin minisrtoci da gwamnoni ya kai naira bilyan 772.2, kuma a yanzu haka EFFC na ci gaba da bincike kan naira bilyan 81.6 wanda ake tsammanin an sace su a ma’aikatar agajin gaggawa da yaki talauci.
Read Also:
Kazalika, kazalika ana zargin wasu dala biliyan biyi da ake zargin sun bata ta hanyar halasta kuɗin haram, wadanda ake tsammanin an karkatar da su ne a baya-bayan nan.
Akwai kuma dala biliyn 2.2 da ake zargin tsohon mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Sambo Dasuki ya karkatar da su, da mai gidajen yaɗa labara nan da ya rasu Raymond Dokpesi; da tsohon gwamnan Sokoto Attahiru Bafarawa: Tsohon ministan kudi Bashir Yuguda da sauransu.
A cewar EFCC kudaden an ware su ne domin sayan makamai da za su taimakwa yaƙin da ake da ‘yan tada ƙayar baya, amma aka sace su aka karkatar da sy aka kashe ba ta hanyar da ta dace ba.
Yayin da Dasuki ke a tsare a DSS a 2015, EFCC ta kama Dokpesi da Bafarawa da Yuguda da dai sauransu..
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 21 minutes 17 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 2 minutes 42 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com