Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru biyar, kan tsohon dan majalisar Bagwai da shanono honarabul Farouk Lawan, bisa samun sa da laifin cin hanci na dalar amurka dubu dari biyar ($500,000).
Kotun Kolin ta tabbatar da Hukuncin Kotun kasa ne, wadda ta yankewa Farouk Lawan hukuncin zaman gidan yari na shekaru biyar, saboda samun sa laifin yana karbar cin hancin dala dubu dari biyar ($500,000), daga hannun wani dan kasuwa Femi Otedola.
Tunda fari dai an zargi Lawan da karbar cin hancin dala dubu dari biyar ($500,000) ne, a lokacin da majalisa take binciken tallafin man fetur a shekarar 2012.
Farouk Lawan dai ya daukaka karar ne tun a watan fabarairun shekarar 2022, inda ya roki kotun kolin ta soke hukuncin kotun daukaka karar dake Abuja, wadda tayi masa daurin shekaru biyar a gidan yari kan laifin farko, inda ta wanke shi akan sauran zarge-zargen guda biyu, wadanda gwamnatin Tarayya tayi kararsa akan zarge-zargen masu alaka da cin hanci da karbar rashawa.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 19 hours 24 minutes 50 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 21 hours 6 minutes 15 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com