Kotun koli ta tabbatar da zaɓen Ahmed Aliyu na jam’iyyar APC a matsayin halastaccen gwamnan jihar Sokoto.
Kotun koli a wani mataki na bai ɗaya ta yi watsi da ƙarar da Sa’idu Umar na jam’iyyar PDP ya shigar na ƙalubalantar nasarar Aliyu a zaɓen gwamna da aka gudanar a watan Maris na 2023.
wani labarin Kotun koli ta yi watsi da ɗaukaka karar da Tonye Cole, ɗan jam’iyyar APC ya shigar in da yake ƙalubalantar nasarar Siminalayi Fubara na jam’iyyar PDP a Zaɓen gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris na 2023 a jihar Rivers. Kotun ta tabbatar da Fubara a matsayin gwamnan jihar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Kotun ta ce Cole bai tabbatar da zarginsa ba na cewa Fubara bai cancanta tsayawa takarar ba saboda bai bai yi murabus daga mukamin babban akanta janar na jihar Rivers ba kafin zaɓen wanda hakan ya saɓawa dokar zaɓe. Kotun ta ce karar da aka shigar bai yi nasara ba kuma ta yi watsi da shi.
haka kuma a wani labarin Kotun kolin ta tabbatar da zaɓen Agbu Kefas na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Taraba.
Kotun kolin a wani mataki na bai daya ta yi watsi da daukaka karar da Farfesa Yahaya Sani na jam’iyyar NNPP ya yi kan rashin cancantar Kefas tsayawa takarar gwamnan jihar.
PRNigeria Hausa












