Ya kamata a cire tallafin wutar Lantarki a Nijeriya – IMF

Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF, ya shawarci gwamnatin shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, da ta cire tallafin lantarki gaba daya, duk da cewa ‘yan kasar na kokawa da tsadar rayuwa, bayan tallafin mai da gwamnatin ta cire a watan Mayun 2023.

A cewar wani rahoto da IMF ya wallafa a shafinsa na yanar gizo, yace gwamnatin Najeriya tana tursasa kanta kan abubuwan da suka neman fin karfinta, don haka akwai bukatar ta janye tallafin lantarki kamar yadda ta cire na man fetur.

Cibiyar ta Bretton Woods ta bayar da wannan shawarar a matsayin hanyar da Najeriya za ta bi domin farfado da tattalin arzikin kasar da ya shiga wani hali, abin da ke zuwa daidai lokacin da gwamnatin kasar ta ce tallafin wutar lantarki tsakanin watan Janairu zuwa Satumban 2023 ya lakume Naira biliyan 375.8, yayin da masu amfani da wutar lantarki suka biya jimillar naira biliyan 782.6.

IMF ya yabawa gwamnatin Najeriya kan sauye-sauyen da ta aiwatar zuwa yanzu amma ta sake nanata cewa ya kamata a cire tallafin lantarki kamar yadda aka cire a bangaren man fetur.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 14 hours 30 minutes 36 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 12 minutes 1 second

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com