Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga Gwamnatin Tarayya data duba halinda Al’ummar Nigeria suke ciki na tsananin kunci kan hauhawar kayan abinci da rashin zaman lafiya a arewacin Kasar.
Read Also:
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren masarautar Kano Abubakar Balarabe kofar Na’isa ya sanyawa hannu kuma aka raba ga manema labarai a jihar Kano
Alhaji Aminu Ado Bayero ya kara da cewa Senator Remi tayi kokari wajan fadada aikinta na alheri da takeyi a jahar kano dubada yawan Al’ummar da jihar take dasu.
Da take nata jawabin Uwar gidan Shugan kasar ta bayyanawa sarkin cewa tazo jihar kano ne domin tagodewa Al’ummar jihar bisa goyon bayan da suka bawa mijinta a lokacin zabe.
Daga karshe tayi alkawarin isar da sakon al’ummar Kano da Arewacin Nijeriya ga mai gidannata.
Uwar gidan shugaban kasar Senator Remi Tinubu tasamu rakiyar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa na kasa Senator Barau Jibrin da Gwamnan jihar Benue da matar shugaban majalisar wakilai na kasa da Uwar gidan Gwamnan Kano.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 34 minutes 4 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 15 minutes 29 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com