Rahotannin daga jihar Sokoto na bayyana cewa wasu ‘yan bindiya dauke da makamai sun kai hari kauyen Gidan Bakuso da ke yankin karamar hukumar Gada a jihar da ke arewa maso yammacin Najeriya, tare da sace daliban wata tsangaya.
Dan majalisar tarayyar mai wakiltar yankin, Honarabul Bashir Usman Gorou ya tabbatar wa manema labarai aukuwar harin, inda ya ce kimanin dalibai 15 ne ‘yan bindigar suka sace, da wasu mata hudu.
Ya ce maharan sun far wa garin ne da tsakar daren ranar Juma’a lokacin da daliban ke barci.
Honarabul Gorou ya ce daliban almajirai ne da ke karatu a makarantar Allo wadanda shekarun suka kama daga takwas zuwa 14.
”Baya ga daliban tsangayar, dan majalisar ya ce a yanzu haka akwai fiye da mutum 63 a yankin da ke hannun ‘yan bindiga, to amma wannan shi ne karo na farko da ake sace kananan almajirai a yankin”, in ji dan majalisar.
Read Also:
Kakain rundunar ‘yan sandan hihar, ASP Ahmad Rufa’i, ya shaida wa BBC cewa kawo yanzu rundunar ba ta samun labarin ba, amma ta aike da jami’ata zuwa yankin don tabbatar da ainihin abin da ya faru.
Yana mai cewa zai tuntube mu da zarar ya kammala tattara bayanai daga wurin jami’ansu da ke yankin.
Harin dai na zuwa ne a yayin da yau da rana wamnatin jihar ta kaddamar da jami’an sa kai na tsaro don magance matsalar tsaron a jihar.
A baya-bayan nan ‘yan bindiga sun zafafa kai hare-hare tare da sace mutane masu yawa a wasu yankunan arewacin Najeriya.
Ko a ranar Alhamis da ta gabata ma wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka kai hari makarantar furame da karamar sakandiren Kuriga a jihar Kaduna, tare da sace daliban makarantar kimanin 287.
Haka ma makon da ya gabata wasu mahara suka sace wasu mutane mazauna sansanin ‘yan gudun hijira fiye da 100 galibinsu mata da kananan yara a lokacin da suke neman itacen girki a garin Gambouro Ngala a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin kasar.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 32 minutes 1 second,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 13 minutes 26 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com