‘Yan bindiga masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa sun yi garkuwa da mutam 61 a kauyen Buda dake karamar hukumar Kajuru, a jihar Kaduna dake ARewa maso yammacin Nijeriya.
jaridar PUNCH ta ruwaito cewa ‘yan bindiga sun shiga garin ne da misalin karfe 11:45 na daren ranar litinin inda suka yi garkuwa da mutane.
Read Also:
kawo yanzu dai rundunar ‘yan sandan jihar basu ce komai ba kan lamarin, sai dai mazauna kauyen sun bayyanawa jaridar yadda lamarin ya faru.
wani mazaunin kauyen Dauda Kajuru, yace masu garkuwar da mutane domin karbar kudin fansa sun yiwa garin tsinke inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi.
“Akwai ‘yan uwa na cikin wadanda suka yi garkuwa da su a jiya, sai dai labarin da muke samu a safiyar nan da ‘yan bindiggar da wadanda aka yi garkuwa da su din sun isa inda suka nufa,” cewar Manyu.
yace tun bayna da aka cire kwamandan rundunar soji da aka fi sani da (Tega) ayyukan ‘yan bindiga ya cigaba da karuwa a kauyukan karamar hukumar Kajuru.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 34 minutes 49 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 16 minutes 14 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com