Home Labarai ‘Yan sanda a jihar Kaduna sun tabbatar da sake sace mutane a...

‘Yan sanda a jihar Kaduna sun tabbatar da sake sace mutane a Jihar

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum fiye da 80 a garin Kajuru dake jihar Kaduna a arewa maso yammacin Nijeriya  a wani sabon hari da suka kai garin ranar Lahadi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Mansur Hassan ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai sai dai bai fayyace yawan adadin wadanda akayi garkuwa da su din ba.

 Hassan ya ce nan ba da jimawa ba za su sanarwa da manema labarai da jama’a iya adadin mutanen da aka sace kasancewar har yanzu ana tantancewa.

“Eh, gaskiya mun samu wannan labari na masu garkuwa da mutane sun sake sace mutane da dama, amma har yanzu ba a san iya adadin mutanen da aka sace ba saboda daji ne gurin.” in ji Hassan

“Shiyasa kullum muke kira ga jama’a da cewa duk lokacin da suka ga gittawar waɗannan mutanen, ba sai laile sun kai hari ba, a yi ƙoƙari a sanar da mu saboda irin waɗannen wurare daji ne sosai”

“Saboda kusan yaƙin da ake yi da waɗannan ƴan ta’adda da kusan jama’an gari ake yi.

Hassan ya ce rundunar jihar ta tura ƙarin jami’an tsaro don bin sawun mutanen da aka ƙara sacewa.

Harin dai na zuwa ne ƙasa da kwana biyu bayan an sace wasu mata fiya mata 15 tare da wani namiji ɗaya a ƙauyen Dogon Nama duk dai a ƙaramar hukumar ta Kajuru.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp