Kotu a jihar Kano ta yanke hukuncin rataya ga dan Chaina da hallaka Ummita.

Wata kotu a jihar Kano ta yanke wa ɗanƙasar China Frank Geng Quarong hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe budurwarsa, Ummukhulsum Sani Buhari.

Kwamishinan shari’a na jihar Kano, Haruna Dederi ne ya tabbatar wa BBC hukuncin kotun bayan zaman shari’ar da aka yi ranar Talata.

Ana zargin ɗanChina da daba wa marigayiyar wuƙa a gidansu da ke unguwar Janbulo a Kano, a ranar 16 ga Satumban 2022.

Laifin kisan ya saɓa da sashe na 221(b) na dokar ‘Penal Code’.

idan dai za’a iya tunawa tun lokacin tsohon gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje, yasha Alwashin tabbatar da ganin shari’a ta yi aikinta a batun shari’a hallaka Ummulkhairi sani Buhari, matashiyar da dan Chaina ya hallaka.

Ya ce tuni suka sa aka kama mutumin da ake zargi Mista Geng Quanrong, bayan mutane sun damke shi a gidansu marigayiyar.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 11 hours 59 minutes 11 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 13 hours 40 minutes 36 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com