Home Labarai Gwamnatin Nijeriya na neman ‘yan kasar da suka ci bashin ta

Gwamnatin Nijeriya na neman ‘yan kasar da suka ci bashin ta

Babban bankin Najeriya CBN ya ce har yanzu wasu ‘yan kasar da suka karbi bashinsa lokacin annobar murar mashako ta korona suka gaza biya.

A wani rahoto, babban bankin na Najeriya ya ce yana bin mutanen fiye da naira biliyan 260.

Babban bankin ya ce daga cikin naira biliyan 419.42 da bankin ya fitar domin bayar da rancen, naira biliyan 41 da miliyan 39 ne kawai jama’a suka biya, inda kuma aka samu kudin ruwa na naira miliyan 174 da dubu 600.

Kuma abin da hakan ke nufi shi ne akwai fiye da naira biliyan 378 da mafiya yawan wadanda suka ci bashin ba su biya ba.

Rahoton ya kara da cewa kowane mutum daga cikin wadanda suka ci bashin, ya amfana da naira miliyan biyu da rabi.

Dangane kuma da fa’aidar da rancen ya yi ga wadanda suka ci gajiyarsa, bankin ya ce shirin, ya samar da ayyukan yi fiye da miliyan daya da rabi a fadin Najeriya.

Bayan annobar Korona ne dai gwamnatin Najeriya ta hanyar babban bankin kasar, ta fitar da makudan kudade domin bai wa ‘yan kasar rance kasancewar sana’ao’i da jari sun lalace a lokacin kullen annobar.

An kuma aiwatar da Shirin ne ta hanyar bankin bayar da rance ga masu kanana da matsakaitan sana’ao’i na NIRSAL.

To sai dai kuma a daidai lokacin da babban bankin ke son a kawo karshen shirin yanzu, fiye da rabin kudaden sun makale a hannun wadanda suka ci bashin.

To amma rahoton babban bankin ya bayar da shawarar cewa za a iya karkata akalar Shirin ta koma karkashin Shirin kanana da matsakaitan sana’ao’i masu alaka da noma domin cigaba da shirin a kuma tabbatar da cewa jama’a sun biya kudaden ko da bayan kammala Shirin ne.

Masana tattalin arziki da masu lura da al’amura dai na ganin beken babban bankin, kasancewar a lokacin da ya bayar da rancen bai yi wa al’ummar kasar cikakken bayanin cewa kudin rance ne ba kyauta ba.

Harwayau, kasancewar wadanda suka ci gajaiyar sun yi hakan ne ta hanyar wasu shugabannin siyasa, ya sa mutanen suka yi tunanin kudin na bulun ne.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp