Shugaban jam’iyyar APC mai mulki a Nigeria, Abdullahi Umar Ganduje, ya zargi gwamna Abba Yusuf na jihar Kano da yin amfani da wasu dabaru wajen fakewa da boye gazawarsa da rashin tabuka komai ga al’umma tun da ya shiga Ofis.
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Edwin Olofu, ya fitar ranar juma’a.
Ganduje yayi Martani ne kan wasu kwamitoci da gwamnatin jihar kano ta kafa domin bincikar yadda Ganduje ya yi tusarrafi da kudaden al’umma da kuma yadda aka yi ta fadan Siyasa a zamanin mulkinsa wanda har yayi asarar rayukan al’umma.
“A gaskiya babu wani abun azo a gani a jihar kano da gwamnan yayi da kudaden da gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu take turowa jihar kano”.
Ganduje ya kuma mayar da martani ne kan matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka na gurfanar da shi a gaban kotu bisa zarginsa da karbar cin hancin dala 413,000, da kuma Naira biliyan 1.38.
Read Also:
“Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta dage dole sai sun shafa min kashin kaji ni da Iyalaina, sai dai sun ƙasa ganewa cewa komai ana yin sa ne akan doron doka da oda” inji shi
“Sun kasa daukar matakin shari’a kan umarni da babbar kotun tarayya da ke Kano ta bayar kwanan nan, inda ta ce laifin da ake zargina da shi, laifi ne da gwamnatin tarayya ce take da hurumi, wanda babban lauyan gwamnatin tarayya da kuma hukumar EFCC ne kadai zasu iya gurfanar da ni akan shi”.
“Har yanzu suna da damar komawa kan tsarina na ci gaba mai dorewa wanda zai ciyar da jihar Kano gaba. Har yanzu bai makara ba don su yi koyi da ci gaban da na samar.”
Ganduje wanda ya mulki jihar a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023, ya kuma bayyana matakin da gwamnatin ta dauka na kafa kwamitoci biyu da za su gudanar da bincike a kansa kan zargin almubazzaranci da dukiyar al’umma da tashe-tashen hankula na siyasa da kuma bacewar mutanen a jihar a matsayin abin farin ciki.
Yace zai fi dacewa da cigaban jihar gwamnatin ta tsawaita wa’adin gudanar da binciken daga 1999 zuwa yau.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 13 hours 58 minutes 46 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 15 hours 40 minutes 11 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com