Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta ce zata sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje bisa zargin almundahana da almubazzaranci da dukiyoyin al’umma.
Shugaban hukumar, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ne ya bayyana hakan a yayin wata ganawa da gidan talabijin na Channels Television ta cikin shirin (Sunrise Daily).
“Yanzu haka da nake magana da ku, muna kan binciken wasu kudin har kimanin N51.3bn wadanda gwamnatin tarayya ta turowa kananan hukumomi kuma aka dauke su daga asusun gwamnati aka aika wa wasu mutane, kuma mun gano mutanen da aka turawa kudin.”
Magaji ya yi zargin cewa a watan karshe na gwamnatin Ganduje ta kwashi Naira biliyan 1 daga asusun gwamnati, da sunan za’a yi aikin hanya da su, amma sai muka ga an tura da kudin ga wasu kamfanonin Chanji Kudaden kasashen waje.
Read Also:
“Muna da wata kara da muka shigar akan Naira biliyan 4, wadda aka fitar da ita daga asusun ajiyar kudaden shiga na jihar Kano zuwa wani kamfanin noma. Duk wadannan kararraki suna gaban kotu,” inji shi.
Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na Kano, wanda ya ce ana kallonsa a matsayin “mai taurin kai” saboda harkar halasta kudaden haramun batu ne da gwamnatin tarayya ce da hurumi akai, amma yace hukumarsa na da hakkin bincike akan zargin almundahana da ake yiwa Ganduje .
Magaji yace ya fara binciken gwamnatin Ganduje ne tun yana gwamnan Kano. Ya ce bai kamata a samu shafaffu da mai a yaki da cin hanci da rashawa a jihar ba.
“Abun dadin shi ne kyawun a Najeriya ba Wanda ya Isa yace yafi karfin a gurfanar da shi a gaban Shari’ar don haka kawai Ganduje ya shirya gurfana a gaban kotu domin ya kare kansa.”
Idan za’a iya tunawa kadaura24, gwamnatin jihar kano za ta gurfanar da Ganduje a ranar Laraba 17 ga Afrilu, 2024, bisa tuhumar da ake masa na cin hanci da rashawa, karkatar da kudade, da almubazzaranci da wasu kudade da suka hada da zargin karbar cin hanci da rashawa $413,000 da kuma N1.38bn.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 29 minutes 36 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 11 minutes 1 second
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com