EFCC ta Gargadi masu shige mata hanci

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta yi kira ga jama’a  cewa laifi ne a hana jami’an hukumar gudanar da ayyukansu na halal.

Wannan na cikin wata sanarwar da Shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar, Dele Oyewale ya sanyawa hannu, inda ta ambaci Sashi na 38(2) (a) (b) na dokar kafa hukumar EFCC wanda ya sanya laifin hana jami’an hukumar gudanar da ayyukansu na halal, wanda kuma ya karya wannan doka ka iya fuskantar daurin kurkuku na kasa da shekaru biyar.

Wannan gargadin ya zama dole bisa ga yadda mutane da kungiyoyin da Hukumar ke bincike ke kara ta’azzara na daukar doka a hannunsu ta hanyar daukar ‘yan baranda domin dakile ayyukan EFCC.

A lokuta da dama, jami’an Hukumar sun yi taka-tsan-tsan wajen tunkarar irin wannan tada zaune tsaye domin gujewa tabarbarewar doka da oda. Abin takaici, ana ɗaukar irin wannan halin a matsayin alamar rauni.

Don haka hukumar ta yi gargadin cewa daga yanzu ba za ta lamunci duk wani yunkurin wani mutum ko kungiya na kawo cikas ga ayyukanta ba domin kuwa za a fuskanci hukuncin da ya dace.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 4 hours 34 minutes 50 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 6 hours 16 minutes 15 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com