Home Labarai Gwamna Kano ya rantsar da sabbin kwamishinoni a jihar

Gwamna Kano ya rantsar da sabbin kwamishinoni a jihar

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jagoranci rantsar da sabbin kwamishinoni guda hudu tare da bayyana ma’aikatan da za su fara aiki.

Gwamna Yusuf ya jagoranci rantsar da sabbin Kwamishinonin ne a dakin taro na Africa House dake gidan gwamnatin jihar kano.

Gwamnan ya bayyana Mustapha Rabi’u kwankwaso a matsayin kwamishinan ma’aikatar matasa da wasanni, sai Abduljabbar Garko a matsayin kwamishinan kasa da safayo na jihar kano, yayin da aka tura Shehu Aliyu yarmedi a matsayin kwamishinan aiyuka na musamman sai Adamu Aliyu kibiya kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar.

Gwamna Yusuf ya Kuma ja hankalinsu da su zama masu gaskiya da rikon Amana a dukkannin al’muransu na yau da kullum.

Ya kuma bukace su da su maida hankali wajen bashi damar sauke nauyin da al’ummar jihar kano suka dora masa.

Idan za’a iya tunawa majalisar dokokin jihar kano tun a watan da ya gabata ne ta kammala aikin tantance sunayen sabbin Kwamishinonin da gwamnan ya tura mata  domin nada su a matsayin Kwamishinoni.

Duk dai a wannan rana gwamnan ya jagoranci rantsar da sabbin masu bashi shawara da suma majalisar dokokin jihar kano ta sahalle masa ya nada su.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp