Rahotanni daga Nijeriya na bayyana cewa farashin gas din girki (LPG) ya fara sauka a kasar sakamakon faduwar darajar dala da habakar darajar Naira a kasuwar kasar.
Idan dai za a iya tunawa a ‘yan tskanin nan AL’ummar Nijeriya suka koka kan yadda farashin Iskar gas din tayi tashi gwauron zabi, abin da suka bukaci mahukunta a kasar da su sanya baki domin ganin an sami sauki.
Read Also:
Ko dai a watan Maris din daya gabata an sayar da gas din na girki a kan farashin Naira 1,500 ko wannen (kg), sai dai sakamakon faduwar dalar a kasuwar chanjin Nijeriya yasa yanzu haka ake sayar da iskar gas din kan farashin Naira 1,100.
Jaridar Economic confidential ta rawaito cewa a wajen sayar da iskar Gas na Iju-ishaga dake jihar Legas ana sayar da iskar gas din naira 1,100 dukkan (kg) an sami ragi kan yadda aka sayar a watan Maris din daya gabata.
Ana dai sa ran farashin zai cigaba da sauka idan babban bankin kasar ya cigaba da kokarin da yake na farfado da darajar Naira a kasuwar chanji ta duniya, tare da sanya idanu kan ‘yan kasuwa wadan ake zargi da tsawwala AL’ummar kasar.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 38 minutes 53 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 20 minutes 18 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com