Home Labarai An janye ‘yan sandan dake gadin Yahaya Bello

An janye ‘yan sandan dake gadin Yahaya Bello

Babban Sufeto ‘yan sandan Najeriya IGP Olukayode Egbetokun, ya bayar da umarnin janye dukkan jami’an ‘yan sandan da ke gadin tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello.

Wannan na kunshe ta cikin wata takar da mai dauke da adireshin hedkwatar ‘yan sandan Najeriya da aka aika zuwa MOPL 37 a Lokoja.

Takardar mai lamba: “CB:4001/DOPS/PMF/FHQ/ABJ/VOL.48/34 ta bayyana cewa, “babban Sefeton ‘yan sandan Nijeriya ya ba da umarnin janye dukkan ‘yan sandan da ke raka tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello.

Idan za’a iya tunawa a ranar Alhamis din da ta gabata ne Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), a wata takarda da ta fitar ta sanya tsohon Gwamnan cikin jerin sunayen wadanda zasu fara farauta.

Wannan dai ya biyo bayan rashin nasarar da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta yi na kama Yahaya Bello a gidansa da ke Abuja, sakamakon zarginsa da ake da karkatar da kudade har N80.2billion.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp