Gwamnatin Yobe ta musanta mutuwar mutane 200 sakamakon cutar Sankarau

Gwamnatin jihar Yobe ta ce sankarau ta kashe mutane 85 tsakanin Janairu da Afrilu sakamakon ɓarkewar cutar a jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Muhammad Lawan Gana ne ya tabbatar da hakan a wani taron manema labarai a birnin Damaturu.

Ya ƙaryata rahotannin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta da ke cewa cutar ta yi ajalin sama da yara 200 cikin mako biyu inda ya ce haƙiƙanin adadin shi ne 85.

Ya kuma ce fiye da marasa lafiya 2,510 da suka kamu da cutar a jihar sun samu sauƙi kuma an sallame su daga asibiti.

Dakta Gana ya kuma ce an tura jami’an lafiya na sa kai sama da 200 zuwa sassan ƙananan hukumomin Poyiskum da Fika a wani ɓangare na ƙoƙarin da ma’aikatar take na daƙile cutar.

Ya ce ma’aikatan lafiya sun bi gida-gida domin ganowa tare da tura mutanen da ke da cutar asibiti.

Yankunan arewacin Najeriya na fama da matsanancin zafi a tsukin nan – yanayin da ke haddasa cutar ta sanƙarau.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 19 hours 57 minutes 55 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 21 hours 39 minutes 20 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com