Kwamitin da aka kafa don bincikar gwamnatin Ganduje ya fara aiki

Kwamitin bincike da gwamnatin Kano ta kafa domin binciken batun zargin wadaƙa da dukiyar al’umma ya fara zamansa na farko.

Kwamitin zai yi bincike ne tsakanin 2015 da 2023, wato zamanin mulkin, Dr Abdullahi Umar Ganduje, inda ake fatan kwamitin zai karɓi ƙorafe-ƙorafe daga jama’a da kuma ‘yan ƙungiyoyi a kan yadda tsohon gwamnan ya yi tasarrufi da kadarorin gwamnati.

A kwanakin baya ne gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamatocin bincike biyu da za su binciki zargin al’mundahana da rikicin siyasa da ɓatan mutane a jihar, al’amarin da ya haifar da zazzafar muhawara.

Kwamitin binciken ƙarkashin jagorancin mai shari’a Faruk Lawan Adamu, ya ce al’umma suna da damar zuwa kwamitin, su gabatar da duk wani ƙorafi ko rashin gamsuwa da yadda aka tafiyar da gwamnatin jihar Kano daga 2015 zuwa 2023.

Barista Bashir Sale mamba ne a kwamitin binciken kuma ya yi wa BBC ƙarin bayani game da farko da kwamitin ya yi.

Ya ce “kadarorin gwamnati – makarantu da filaye da gidaje, maƙabartu da burtali, ya ya aka yi da su? An sayar? bisa ƙa’ida aka sayar? Idan ba bisa ƙa’ida aka sayar ba, wa ya siya, idan kuma ka siya, wa ka siyarwa?

Ya kuma ce za su bi ƙa’ida da yin adalci a binciken da za su yi.

Nan gaba ne kuma za a fara sauraron bahasi daga ɓangarori daban-daban ciki har da duk wanda yake ji an aiwatar da wani aiki a yankinsa da bai gamsu da shi ba.

Akwai kuma kwamitin da zai yi bincike a kan rikice-riciken siyasa da mutanen da suka ɓata da tashin hankalin da aka yi a 2015 da 2019 da kuma 2023.

Kafa wannan kwamatocin bincike dai ya haifar da ce-ce-ku-ce da kace-na-ce tsakanin ɓangaren tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da kuma gwamnatin NNPP, inda bangaren Gandujen ke zargin akwai bita-da-ƙulli a binciken da ake ƙoƙarin yi, kasancewar an zaɓi tsohon gwamna ɗaya ne wajen yin binciken, zargin da gwamnatin kwankwasiyya ta musanta.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 18 hours 26 minutes 50 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 20 hours 8 minutes 15 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com