Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta sami nasarara kama mutane 28 da ake zargi da Damfara a birnin tarayya Nijeriya Abuja.
Wannan ya biyo bayan wani simame da dakarun hukumar dake shiyyar birnin tarayya suka gudanar kan wadanda ake zargin da ayyukan damfarar ta yanar gizo.
Read Also:
Ta cikin wata sanarwa da sashin yada labarai da hulda da jama’a na hukumar ya fitar, yace an sami nasarar kama mutanen ne a yankin Gwarimpa da Katampe dake birnin bayan samun bayanai kan yadda suke gudanar da ayyukan na damfara.
Sanarwar ta kara da cewa dakarun sun sami wayoyin hannun guda 43 kirar kamfanoni da dama sai kuma abin hawa da kuma agoggunan zamani (Smart watches) a hannun wadanda ake zargin.
Daga bisani hukumar ta tabbatar da shirin ta na gurfanar da su gaban kotu da zarar ta kammala bincike.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 53 minutes 4 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 34 minutes 29 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com