Home Labarai Sojojin Nijeriya sun dakile harin ‘yan Bindiga a Adamawa

Sojojin Nijeriya sun dakile harin ‘yan Bindiga a Adamawa

Dakarun sojojin Najeriya da ke yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabashin kasar tare da rundunar haɗin gwiwar sojoji da ƴan sa-kai sun yi nasarar kame wasu gungun ‘yan ta’adda da ke kan hanyarsu ta kai hari a karamar hukumar Yola ta Kudu a jihar Adamawa.

ta cikin wata wallafa da Rundunar sojin Najeriyar ta yi a shafinta na X, ta ce dakarunta sun ci karo da ƴan ta’addar da ke shirin kai wa al’ummar hari ne a lokacin da suke sintiri a kusa da Wuro Jabbe.

Ta kuma ce anyi zazzafar musayar wuta tsakanin sojojin da ƴan ta’adda abin da ya tilasta wa ‘yan ta’addan mika wuya tare da barin makamansu. Sojojin sun kuma ƙwace makamai da harsasai 402.

A wani samame na daban kuma amma mai alaka da wannan, sojojin sun ce sun kama wasu mutane uku da ake zargi da harbin bindiga a yankin Sukuk, da ke karamar hukumar Madagali ta jihar. An kama waɗanda ake zargin da makamai da dama.

Sojojin Najeriya na ci gaba da taka-tsan-tsan tare da jajircewa wajen samar da zaman lafiya da tsaro a yankunan ƙasar.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp