Rundunar sojin Najeriya ta bankaɗo haramtattun matatun mai 50 a dajin Biseni da ke ƙaramar hukumar Yenagoa a jihar Bayelsa, a yankin Neja Delta mai arzikin man.
Kwamandan rundunar haɗin gwiwa ta Operation Delta Safe a yankin, Rear Admiral John Okeke wanda kuma ya jagoranci samamen ne ya bayyana haka.
Read Also:
Okeke a yayin da yake magana da ƴan jarida ya ce a ranar 9 ga watan Mayu, sun kai samame ƙaramar hukumar Ukwa ta Yamma da ke jihar Abia kan iyaka da Rivers, ya kuma ce za su ci gaba da kai irin wannan samame domin gano wasu matatun mai da ake gudanar da su ba bisa ƙa’ida ba.
A cewarsa, sun gano wani rami da aka haƙa a ɗaya daga cikin haramtattun matatar mai wanda ke iya ɗaukan manyan motoci 10 maƙare da duro-duro na iskar gas inda kuma suke ajiye ɗanyan mai wanda daga nan kuma su riƙa shigar da shi wurin girke-girkensu.
Rear Admiral John Okeke ya ƙara da cewa za su ci gaba da kai irin wannan samame domin fatattakar masu fasa-ƙwabrin mai a yankin na Neja Delta.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 19 hours 32 minutes 50 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 21 hours 14 minutes 15 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com