Majalisar Dattijan Nijeriya ta bukaci Gwamnatin tarayyar kasar data ci gaba da biyan naira dubu 35 matsayin mafi karancin albashi a kasar, kasancewar ba’a cimma matsaya kan Karin mafi karancin Albashin.
Read Also:
Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio ne ya bayyana hakan a karshen ganawar sa’oi 4 tsakanin kungiyoyin kwadagon da wakilan gwamnatin tarayya bisa shirin kungiyoyin na tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.
Akpabio ya kuma roki kungiyoyin na kwadago da su jenye yajin aikin saboda ‘yan Nijeriya da ci gaban kasar.
Sai dai ministan yada labarai da wayar da kai Alhaji Muhammad Idris, yace matsayar gwamnatin shine zata cigaba da biyan tsohon albashin har sai tattaunar ta kammala.
PRNigeria Hausa