Gwamnatin Nijeriya tace ‘yan Nijeriya zasu wahala saboda yajin aikin NLC da TUC

Ministar ƙwadago ta Najeriya, Nkeiruka Onyejeocha, ta ce ƴan ƙasar zasu sha wuya idan har ƙungiyar ƙwadago ta NLC, ta kafe kan ci gaba da yajin aikin da suka kira.

ta bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da ita a tashar talabijin ta Channels, bayan da shugabannin ƙwadagon suka jagoranci yajin aiki na sai baba ta gani daga ranar Litinin, a kan maganar mafi ƙanƙantar albashi a Najeriya.

Ministar ta ce tana fatan za a samu matsaya a kan batun albashin, amma tafiya yajin aiki abu ne da ke tattare da illoli ga tattalin arziƙin ƙasa da kuma rayuwar jama’a.

Onyejeocha ta ce, ”idan yajin aikin ya ci gaba, ƴan ƙasa za su wahala, kuma tuni ma har sun fara wahala. Ɗalibanmu da ya kamata su rubuta jarrabawa lamarin ya shafe su saboda sun rasa ababen hawa da za su je wuraren jarrabawar.”

Ta ƙara da cewa, ”akwai kuma mutanen da ba su da abin da za su ci sai sun je wuraren aikinsu sun nema. Wasu mutanen da ke aiki a sakatariya kullum sun dogara ne a kan abin da suke samu a ofisoshin.”

”Sannan a ɓangaren yin ayyuka da abubuwa, mun san cewa idan aka dakatar da ayyuka, hakan zai shafe tattalin arziƙinmu,” in ji ministar.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 14 hours 23 minutes 57 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 5 minutes 22 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com