Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) Reshen jihar Adamawa ta sami nasarar kama muggan kwayoyi da nauyin su ya kaia kilogram dubu 4,732.128, tare da dilolin kwayoyi 454 a jihar.
Read Also:
kwamandan rundunar Agboalu Samson na jihar ya bayyana cewa kwace miyagun kwayoyin na zuwa ne a wani bangare na ranar yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta duniya, kwayoyin da aka sami nasarar kwatowa sun hadar da Cannabis sativa, wato Indian hemp; Methamphetamine ko kuma Ice; Cocaine, Tramadol, Exol-5; Diazepam ; Codeine-ta ruwa; Rohypnol , da kuma allurar Pentazocine.
kwamandan ya kara da cewa kwayoyin da aka kwace sun na wakiltar kashi 75 cikin dari na wadanda hukumar ta kwace a daga watan Yunin 2022 zuwa Mayun 2023.
sai dai a yayin da yake gabatar da jawabin ga manema labarai Kwandan rundunar yace dilolin miyagun kwayoyin sun ragu sosai.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 18 hours 28 minutes 36 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 20 hours 10 minutes 1 second
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com