Gamayyar kungiyoyin Ma’aikatan hukumar dake lura da ayyukan ‘yan sanda ta Nijeriya PSC ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu daya sauke shugaban rundunar ‘yan sandan kasar Kayode Egbetokun bisa yunkurin yin kafar ungulu a shirin daukar jami’an hukumar.
Yayin da take ganawa da manema labarai a birnin Abuja ranar laraba kungiyar ta zargi wasu cikin manyan jami’an hukumar da yunkurin cusa sunayen wadanda basu cancanta ba a lokacin jarabawar daukar aikin.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Mambobin kungiyar dake rera wakokin zanga – zanga, sun bayyana yunkurin rundunar ‘yan sandan na na dauke hankula.
Kungiyar tace NPF na kokarin kare shugaban kasa kada ya fahimci rashin shirin makarantun horar da ‘yan sanda da yadda suke a mawuyacin hali.
Wannan dai na zuwa ne bayan da hukumar dake lura da ayyukan ‘yan sanda ta saki sunayen mutum dubu 10 wadanda suka sami nasarar haye jarabawar daukar aikin dan sanda a Nijeriya.
Sai dai daga bisani hukumar ‘yan sandan ta yi fatali da jerin sunayen wanda tace akwai ayyukan damfara a cikin sa.
PRNigeria Hausa











