Gwamnatin jihar Sokoto ta musanta zargin cire mai alfarma sakin musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III,
Wannan na cikin wata sanar wada mai Magana da yawun Gwamnan jihar Abubakar Bawa ya fita aka raba ta ga manema labarai, sanarwar kuma bukaci Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima ya rika bincike kafin yin sharhi kan duk Wani Labari da ya gani a kafofin sadarwa na zamani.
“Munyi zaton mataimakin shugaban kasa ya tuntubi Gwamnan Jihar sokoto kafin ya fito fili yayi magana akan Batun Tsige Sarkin Musulmi.
Read Also:
“gaskiyar magana ita ce, ba’a taba yunkurin tsige Sarkin ba, haka kuma ba mu aika masa da wata barazana ba dangane da hakan ba a cewar Sanarwar”
Sanarwar ta kara da cewa, Sarkin Musulmi na cin moriyar duk wani ikon da yake da shi, ba mu taba tauye masa wani ‘yanci ko hakkinsa ba”
Haka Gwamnati da al’ummar Jihar Sokoto na girmama Majalisar Sarkin Musulmi kuma zasu yi duk mai yiwuwa don kare martabar wannan Masarautar”.
“Daga bisani gwamnati na tabbatarwa ‘yan Nijeriya cewa, za ta cigaba da kare Majalisar Sarkin Musulmi da mutuncinta a kowane lokaci”
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 59 minutes 49 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 41 minutes 14 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com