Kotun tarayya ta rushe kwamitin dake bincikar Ganduje a Kano

Mai shari’a Simon Amobeda na babbar kotun tarayya dake zaman ta a Kano, ya baiwa Justis Faruk Adamu da Mai shari’a Zuwaira Yusuf, alkalan babbar kotun jihar Kano wa’adin sa’o’i 48 da su yi murabus daga shugabancin kwamitin binciken almundahana da kadarorin gwamnati da kuma tashe-tashen hankula na siyasa, wadanda gwamnatin jihar kano ta kafa.

Da yake yanke hukunci a ranar Alhamis a karar da tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya shigar, mai shari’a Amobeda, ya ce hukumar ta kula da harkokin Shari’a ta kasa zata dakatar da biyan duk wani albashi da alawus-alawus da ake yi biyan alkalan biyu daga hadakar asusun shigarta idan har suka gaza bi umarnin kotun.

idan za’a iya tunawa a ranar 4 ga watan Afrilu ne Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da kwamitocin binciken shari’ar guda biyu karkashin jagorancin Mai Shari’a Adamu da Yusuf, domin gudanar da bincike a kan almubazzaranci da dukiyar jama’a, tashe-tashen hankulan siyasa da kuma wadanda suka bace daga shekarar 2015 zuwa yanzu. 2023.

Mai shari’a Amobeda ya bayar da umarnin cewa alkalan su daina gudanar da ayyukan zartarwa da gwamnan ya ba su a cikin kotuna wanda ke nufin yanke hukunci a tsakanin mutane da hukumomi a jihar.

Kotun ta kuma bayyana cewa gwamnan ba shi da hurumin nadawa da kuma rantsar da su a matsayin shugabannin hukumar bincike, ofishin da ya kamata kwamishinoni su gudanar da shi.

Kotun ta kuma bayyana cewa, duba da hukuncin da Mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman ya yanke na cewa EFCC da ICPC ne kawai za su iya bincikar tsohon gwamnan, ya ce abun da gwamnan ya yi na kafa kwamitin da zai binciki tsohuwar gwamnatin mai kara cin fuska ne a ga alfarmar bangaren Shari’a.

PRNigeria Hausa

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 6 hours 18 minutes 13 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 7 hours 59 minutes 38 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com