Home DUNIYA Rundunar ‘yan sanda Kano tayi holen bata gari 149 a jihar

Rundunar ‘yan sanda Kano tayi holen bata gari 149 a jihar

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce ta kama mutum 149 da take zarginsu da ayyukan fashi da makami da daba da garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka cikin kwanaki 10 da suka gabata a jihar.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna ne ya bayyana haka a yayin da rundunar ‘yan sandan ke holen wadanda ake zargin gaban manema labarai bisa kamen da rundunar ta yi.

Ya ce an kama ƴan daba 106 da waɗanda ake zargi masu fashi da makami ne su 25 da mutum biyu da ake zargi suna garkuwa da mutane sai masu satar mota uku da dillalan miyagun ƙwayoyi uku a sassa daban-daban na jihar.

“Mun kuma gano motoci biyu da babura takwas da wuƙaƙe 58 da bindiga ɗaya da ƙunshi 87 na abin da ake zargin tabar wiwi ne.

Kiyawa ya ce kamen ya biyo bayan shawagin da ƴan sanda suke yi a sassan jihar domin hana aikata laifuka.

A cewarsa, mutanen da aka kama na sashen binciken manyan laifuka na rundunar inda ake gudanar da bincike a kan su.

Kwamishinan ƴan sanda na jihar, Salman Dogo Garba ya ce rundunar za ta ci gaba da aiki ba dare ba rana domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp