Rundunar ‘yan sandan jihar jigawa ta tabbatar da mutuwar mutum 2 tare da kone gidaje 3 bisa wata arangama tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar Birnin Kudu dake jihar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
kakaikin rundunar ‘yan sandna jihar DSP Lawan Shiisu Adam ne ya tabbatar da hakan inda yace jami’an ‘yan sandan hadin gwiwa da jami’an tsaron Civil defence da kuma dakarun sa kai na bijilanti. sun sami nasarar kwantar da rikicin tare da kama mutum 5 da kuma shanu guda biyar da aka yasar.
Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa makiyayan da suka fito daga jihar Katsina, sun tasamma yankin da tarin garken shanu, inda suka fara lalata amfanin gonar da manoma suka shuka, wannan ne ya sanya manoman daukar matakin kare gonakinsu da rayukansu.
yace arangamar ta haddasa mutuwar mutum 2 daga ko wanne bangare tare da kone gidaje 3 mallakin alúmmar garin.
PRNigeria Hausa











