Hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arziki kasa ta’annati ta EFCC ta girke jami’an tsaro a bakin ofishinta na jihar legas bisa zargin gudanar da zanga – zanga kan hukumar.
jaridar Emergency Digest ta ruwaito cewa an hangi wasu dakarun kai daukin gaggawa a bakin kofar shiga hukumar take yaki da masu zagon kasar ga tattalin arziki, cikin su kuwa har da jami’an tsaro DSS wadanda suka rufe dukkan hanyoyin shiga ofishin dake hanyar Awolowo dake yankin Ikoyi a jihar.
Read Also:
wannan dai na zuwa ne bayan hukumar ta fallasa wani shiri na wasu gungun mutane dake shirin gudanar da zanga-zanga a kanta.
A ranar Alhamis din data gabata mai magana da yawun hukumar Dele Oyewale, yace bayanan sirri sun tabbatar musu da cewa an shirya gudanar da zanga – zanga kan hukumar wanda kuma tsohon Gwamnan jihar da wasu tsuffin minitoci suke da alhakin hadata kan hukumar ta EFCC.
wani mai anfani da shafin X #PidomNigeria shine ya fara yada wani sako ta cikin wata takar dar sanarwa wanda ya yi mata adreshi zuwa ga shugaban hukumar, Ola Olukoyode a shafin dake bukatar matasa su fito ayi zanga zanga a cikin dare 4 ga watan Yunin 2023.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 10 hours 10 minutes 54 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 11 hours 52 minutes 19 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com