Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana Ranar Litinin matsayin ranara hutu

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusif, ta ayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutun sabuwar shekarar musulunci ta 1446 bayan hijirar fiyayyen halatta Annabi Muhammad (S A W) daga makka zuwa Madina.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Baba Halilu Ɗantiye ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce gwamnatin  zata ci-gaba da samar da managartan tsare-tsare na tallafawa al’umma domin su dogara da kansu.
Haka kuma ta hori al’ummar jihar su yi amfani da ranar hutun wajen yin addu’oin samun zaman lafiya a jihar, dama neman sauƙin rayuwar ƙunchin da ake ciki.
A ƙarshe Gwamnatin ta yi fatan al’umma zasu ci-gaba da yiwa jihar addu’ar samun nasarori dama haɓɓakar tattalin arziƙi.
PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 12 hours 24 minutes 30 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 5 minutes 55 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com