Rumbun wutar lantarkin Najeriya ya sake ɗaukewa a karo na 4 cikin 2024

Kamfanin Dakon Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya tabbatar da sake ɗaukewar wutar lantarki daga rumbun samar da ita na Najeriya a ranar Asabar.

Wannan dai shi ne karo na huɗu da wutar ta ke ɗaukewa gaba ɗaya tun daga farkon wannan shekarar zuwa yanzu.

Wani rahoto da kamfanin ya wallafa a shafinsa na internet ya nuna cewa da misalin karfe 2:00 na yammacin wannan rana an iya samar da wutar da yawanta ya kai megawat 2,797.16, kasa da yadda ake samu a baya, idan an kwatanta da misalin karfe 1:00 na wannan yammaci da ya kai megawatt 3,417.99.

Haka adadin wutar ya sake saka da misalign karfe 3 na yammacin zuwa 1,020.08 inda daga bisani cikin mamaki ya koma 0.80 da karfe.

Ba tun yanzu ba ’yan Najeriya ke kokawa kan yadda rashin wutar lantarki ke haifar musu da tasgaro a harkokin su na yau da kullum.

A bana kaɗai, kasar nan ta fuskanci durkushewar wutar lantarki akalla sau uku, inda matsalar ta faru sau 227 a tsahon shekaru 14 kamar yadda kamfanin dakon wutar lantarkin na TCN ya bayyana.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 12 hours 30 minutes 24 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 11 minutes 49 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com