Home DUNIYA Sojoji na son mutanen Zamfara su rika ba su bayanai don dakile...

Sojoji na son mutanen Zamfara su rika ba su bayanai don dakile ta’addanci

Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, Laftanar-Janar Taoored Lagbaja, ya bukaci al’ummar jihar Zamfara da su rika ba dakarunsu bayanan da za su taimaka musu wajen gano maboyar ’yan ta’addaa jihar.

Lagbaja ya bayyana hakan ne ta bakin kwamandan runduna ta daya da ke garin Gusau, babban birnin jihar.

Kazalika, Babban Hafsan Sojojin ya raba kayan karatu da na sawa ga masu karamin karfi..

Shi ma da yake jawabi a yayin taron, Kwamandan rundunar ta daya wanda ya sami wakilcin Kanal Joseph Umaru, ya ce sun raba kayan ne domin tallafa wa dalibai da kuma masu karamin karfin domin karfafa musu gwiwa a fannin ilimi.

Ya kara da cewa wannan tallafi na matsayin wani bangare na ranar bikin Ranar Sojojin da aka gudanar a jihar wanda ya kunshi ayyukan rundunar da kuma tabbatar da hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp