Home DUNIYA Kotu ta umarci Sadiya Farouq ta yi bayanin yadda ta kashe biliyan...

Kotu ta umarci Sadiya Farouq ta yi bayanin yadda ta kashe biliyan 729 na tallafi

Babbar kotun tarayyar da ke jihar Legas ta umarci tsohuwar ministar jinƙai, Sadiya Umar Farouk, da ta yi bayanin yadda aka kashe naira biliyan 729 na tallafin da aka raba wa talakawan kasar na tsawon watanni shida.

Cikin hukuncin da ya yanke, mai shari’a Deinde Isaac Dipeolu ya kuma umarci tsohuwar ministar ta wallafa sunaye da bayanan mutanen da suka amfana da tallafin da jihohin da aka raba, da yawan kuɗin da aka raba a kowacce jiha.

Ƙungiyar SERAP mai fafutikar yaƙi da cin hanci da rashawa ce ta shigar da karar Sadiya Farouk a gaban kotun, inda ta buƙaci kotun ta tilasta mata bayar da bayanan, kasancewar kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba ta ‘yancin samun bayanan.

Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, mai ɗauke da sa hannun mataimakin daraktanta, Kolawole Oluwadare, SERAP ɗin ta ce ta samu kwafin hukuncin da kotun da yi ranar Juma’a.

Alƙalin kotun ya ce kotu ta tilasta wa tsohuwar ministar bayar da bayanan, kasancewa kundin tsarin mulkin ƙasar ya yi tanadin bayar da bayanai ga kowanne ɗan ƙasa ciki har da SERAP.

”Don haka kotu ta umarci tsohuwar ministar ta yi bayanin yadda ta kashe naira biliyan 729 wajen raba wa talakawan Najeriya miliyan 24.3 a shekarar 2021”, kamar yadda hukuncin ya nuna.

Mai shari’a Dipeolu, ya kuma ce dole ne tsohuwar ministar ta yi wa SERAP cikakkun bayanan hanyoyin da aka bi wajen zaɓo mutanen da suka amfana da tallafin.

Sannan kotun ta kuma umarci ministar ta yi bayanin hikimar biyan naira 5,000 ga talakawan ƙasar miliyan 24.3, wanda adadin kuɗin ya kai kashi biyar cikin 100 na kasafin kuɗin ƙasar na shekarar 2021.

Tun da farko dai lauyan tsohuwar ministar ya buƙaci kotun ta yi watsi da buƙatar ƙungiyar ta SERAP, to sai dai alƙalin kotun bai amince da buƙatar lauyan tsohuwar ministar ba.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Zaɓen 2027: IGP Disu ya Umarci Manyan Jami'ai da su Ƙarfafa Leken Asiri, da Shirye-shiryen Aiki2027: Ƙungiyar TMG ta Bukaci Atiku, Obi, Makinde, Sowore Su Tattauna Kan Ɗan Takara Ɗaya na Hadin KaiGwamnan Enugu Ya Naɗa Mataimaka 1012027: Ƙungiyar OK ta yi Watsi da Haɗakar NDC, ta Sha Alwashin Rike TsarintaMinistan Tsaro ya Jaddada Kudurin Najeriya na Wanzar da Zaman Lafiya a Duniya a Taron UNGA Karo Na 81Hukumar EFCC Ta Sake Bayyana Neman Tsohon Shugaban Fansho Maina Ruwa-a-JalloTinubu Zai Bai wa Mazauna Abuja Manyan Ayyuka Kyautar a Watan Disamba – WikeHukumar Kwastam ta Tantance Kusan Mutane 3,000 Yayin da Aikin Daukar Ma'aikata na 2025 ya KareMazauna Kauye Sun yi Murna Yayin da Sojoji Suka Dakile Harin Ta'addanci, Sun Kwato Shanu a SakkwatoFarashin Canji da Yawa ya ja wa Najeriya Asara Fiye da Tallafin Man Fetur – CardosoGwamnatin Tarayya ta Kaddamar da Kwamitin Bincike Kan Mutuwar Ma'aikatan Haƙar Ma'adinai 37 a Hukumar Kula da Haƙar Ma'adinai ta NSCDCMajalisar Dattawa ta 10 da Ma'anar Jagorancin Majalisa Daga Kabir AkintayoDarakta Janar na NITDA ya yi Kira da a Hada Hannu Kan Tsarin AI a Taron Manyan ShugabanniƳancin Sanin Gaskiya: Bayani Game da Tsarin Gudanar da Harkokin Sadarwa na Najeriya Daga Franklyn Ginger-EkeHOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a Tsare
X whatsapp